ANA ZARGIN SADIYA KABALA DA AUREN BOGI
Idan masu bibiyar mu basu manta ba, a ranar Lahadin da ta gabata ne muka kawo maku labarin auren jarumar Finafinan Hausa mai suna Sadiya Ahmad Kabala.
Inda muka bayyana maku cewa an daura auren ta a ranar Asabar din ta gabata a garin Kaduna.
Kamar yadda muka bayyana maku a labarin, mun yi iya bakin kokarin mu don neman karin bayani game da auren amma abin ya ci tura.
Kwatsam! Sai muka samu kiran waya daga wata majiya mai tushe, wadda ta bukaci a sakaya sunan ta. Inda ta tabbatar mana da cewa Sadiya ba ta yi aure ba.
“Majiyar ta ci gaba da cewa, wanda ta sanya hoton ta da shi, sunan sa Ibrahim Lamido dan jihar Sokoto ne, suna soyayya da shi, kuma ya yi mata alkawarin zai aure ta, amma sai ya fasa. Shi ne ta yi hikimar sanyawa a hada hotunan su a yada a soshiyal midiya a yada a matsayin sun yi aure, wata kila hakan zai sanya ya aure ta. Duk da haka dai hakarta, ba ta cimma ruwa ba, in ji majiyar”.
Daga Kannywoodexclusive
Mun kara iya bakin kokarin mu wajen kira lambar Sadiya Kabala domin amsa tambayoyin mu game da zargin da ake yi mata na auren Bogi, amma ba ta daga wayar mu ba. Mun tura mata sakon kar ta kwana wayar ta, da kum WhatsApp din ta, nan ma ba ta ce komai ba.
© hutudole
Post a Comment