A ranar Litinin ne gwamnatin jihar ta Kano ta sanar da cire Sanusi a matsayin sarkin Kano.
Sakataren gwamnatin jihar, Usman Alhaji ne ya bayar da sanarwar a yayin taron masu zartarwa a jihar.
Ya ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya cire sarkin ne saboda zarginsa da rashin biyaya ga umurni da gwamnatin jihar ke bawa masarautar.
A sanarnar da ta fitar a shafinta na Twitter a ranar Litinin, jam'iyar ta ce an cire sarkin ne a lokacin da bai dace ba amma ta yi kira ga al'ummar jihar su kasance cikin lumana da bin doka .
Wani sashi na sanarwar ya ce: "Cire sarkin Kano:
PDP ta bayyana damuwar ta, ta yi kira ga al'umma su kwantar da hankulan su."
A wani rahoton kun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ta ba Muhammadu Sanusi II gurbin aiki bayan tube masa rawani da gwamnatin jihar Kano tayi a ranar Litinin.
Ta bashi gurbi ne a KADIPA, cibiyar habaka kasuwancin jihar. A wata takar da da ta fito daga gidan Kashim Ibrahim, Gwamna Nasir El-Rufai ya amince da kafa shugabannin cibiyar KADIPA din.
An kafa cibiyar ne a 2015 kuma tana kan gaba ne wajen habaka kasuwancin jihar tare da saukakawa kasuwanci a jihar Kaduna. Bankin Duniya kuwa ya kalla cibiyar a matsayin ta farko a fannin kasuwanci a Najeriya.
Post a Comment