Babban kotun tarayya da ke Abuja a ranar Juma'a ta bayar da umurnin sakin tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II daga inda aka tsare shi a garin Awe na jihar Nasarawa bayan an cire daga kan mulki a ranar Litinin.

Mai shari'ar Anwuli Chikere ne ta bayar da umurnin sakamakon bukatar da shugaban lauyoyinsa, Latee Fagbemi (SAN) ya shigar a ranar Juma'a.

Kotun ta ce a mika takardan umurnin sakin Sanusi da dukkan hukumomin da suka tsare da shi.

Wadanda Sanusi ya yi karar su a kotun kan batun tsare shi suna hada da Sifeta Janar na 'yan sanda, Muhammad Adamu; Shugaban hukumar DSS, Yusuf Bichi; Attony Janar na jihar Kano, Ibrahim Mukhtar da Ministan Shari'a na Najeriya, Mista Abubakar Malami (SAN).

Source: Legit.ng/hausa

©HausaLoaded

Post a Comment

Emoticon
:) :)) ;(( :-) =)) ;( ;-( :d :-d @-) :p :o :>) (o) [-( :-? (p) :-s (m) 8-) :-t :-b b-( :-# =p~ $-) (b) (f) x-) (k) (h) (c) cheer
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.

 
Top