Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da sabbin matakan hana shigowar baki daga kasashen Turai cikin Amurka da zummar yaki da cutar Coronavirus.

 

Sai dai shugaban ya ce, tsauraran matakan ba za su shafi Birtaniya ba wadda ke da mutane 460 da suka kamu da Coronavirus.

 

Trump ya ce, wannan sabuwar doka za ta fara aiki ne a ranar Juma’a, amma ya bayyana cewa, hanin tafiye-tafiyen bai shafi Amurkawa ba.

 

Haramcin zai shafi kasashen Turai na yankin Schengen kadai kamar yadda shugaba Trump ya bayyana.

Mutane 1,135 aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon cutar ta Coronavirus a Amurka, yayin da 38 suka mutu a kasar.

 

Shugaba Trump ya ce, kasashen Turai sun gaza daukar makamancin matakan da Amurka ke dauka wajen yaki da cutar.



© hutudole

Post a Comment

 
Top