Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa wasikar da aka aika mai ta cewa an saukeshi daga mukamin sarkin Kano daga gidan Gwamnatin jihar ba’a rubutata da kyau ba.

 

Sarkin yayi wannan maganane a cikin wani gajeren bidiyo da yayi ta yawo a shafukan sada zumunta inda yake cewa hujjojin da aka bayar cikin Wasikar, cikin sauki zai je kotu kuma yayi nasara.

 

Saidai ya bayyana cewa baya son komawa Sarki yanzu yana son ya ci gaba da fuskantar wasu abubuwan daban na rayuwarsa.

Ga kalaman nasa kamar haka:

 

“Kwata-kwata hujjojin da aka bayar a wasikar ba a rubuta su da kyau ba, abu ne mai sauki in tafi kotu in samu nasara idan ka duba abin da ke cikin wasikar,” in ji shi.

 

“Kotu za ta yi tambayoyi kamar haka; Shin kun tuntube shi? Kun nemi jin ta bakinsa? Kun ba shi dama ya kare kansa? Idan amsoshin a’a ne, shi ke nan za a sami nasara.

“Amma ba zan je kotu ba, gara in fuskanci rayuwa ta gaba kuma.”



© hutudole

Post a Comment

 
Top