Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai, ya bayyana dalilansa na bai wa tsohon sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II mukamai biyu a jihar Kaduna.

 

Ya ce, ya ba tsohon sarkin Kano mukaman ne saboda abokinsa ne tun suna kuruciya, kuma ya kasance yana taimakonsa dan haka shima yake kokarin ya saka wa sarkin da dan abin da zai iya yi.

 

El-Rufa’i, ya ce tsohon sarkin Kano mutum ne mai tarin ilimi da ke da martaba a fadin duniya kuma ya ba shi mukamin na domin jihar Kaduna ta amfana ta kuma samu ci gaba da tarin iliminsa.

Aminiya.



© hutudole

Post a Comment

 
Top