A jiya ne Gwamnatin Tarayya ta kira shugabannin kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, da sauran masu ruwa da tsaki zuwa wani taro mai mahimmanci wanda zai gudana a yau don nemo maslaha.

 

Kiran ya biyo ne ta bakin Ministan Kwadago da Aiki, Dakta Chris Ngige, wanda zaman zai kasance da Ma’aikatar Ilimi da Kudi, da na Hukumar Jami’o’i ta Kasa, NUC.

 

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da majalisar wakilai ta shigar da kudiri domin shiga tsakani don dakatar da yajin aikin da kungiyar ASUU ke ci gaba da yi kan tsarin hada-hadar biyan albashi da na ma’aikatar, IPPIS, da sauransu.

 

Sanarwar ta kara da cewa: ” An gayyaci taron wanda zai gudanane a dakin taro na Ministan kwadago tare da Ma’aikatar Ilimi da Kudi, da na Hukumar Jami’o’i ta Kasa, NUC.”



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top