Ta Tabbata Za a tsayar da shirya film din Hausa Jim kadan bayan bullar tagwayen bidiyoyin tsuraici

Ta tabbata Za a tasayar da shirya film din Hausa Jim kadan bayan bullar tagwayen bidiyoyin tsuraicin jaruman kannywood acikin watan daya gabata,

Wakilin Jaridar Hausatrust ya tattauna da Ciyaman din daraktoci na jahar kano wato Abdullahi Muhammad Nalako Inda yai mana cikakken Bayani akan hukuncin da manyan kungiyoyin masana antar zasu dauka nan bada jimawa ba kan tsayar da harkar film gabaki daya har sai an san wadanda suke cikin wannan masana anta,

Abdullahi Nalako Ya bayyana cewa; bayan zaman da mukai mukayi sakamakon abubuwan da suke faruwa nan da can sai muka ga cewa yakamata muyi Addua Allah mun tuba kayafemu tunda mu yan adam ne

bayan munyi adduoi ne babbar kungiyar mu ta moppan wacce Dr Ahmad Sarari yake wakiltar ta a matsayin shugabanta na arewa to bayan haka sai shi ya bujiro da wasu kudure kudure wanda harda cewar a dakatar da shirya fina finan hausa gaba ki daya har sai mun tsaya mun daidaita kanmu munsan mutanen da suke cikinta,

kuma a hakane zamusan wane mutum meyazoyi cikin wannan masana anta produsa ko daralktane koma me kazoyi zamu sani rashin yin hakan tun farko shine yake jawo mana matsaloli da suke zuwa su damemu

mun tan bayeshi cewar baya ganin a kwanakin baya hukumar censor ta kano tace kowa sai yaje yayi rijista da ita acikinku kuma aka samu wadanda basuje sunyi rijistar nan ba baka ganin yanzu ma zaa iya samun wasu suki bun wannan umar ni sai yace,,

waccan dokace ta senso dayawa wadanda suka ki zuwa suyi rijistar suna kawo dalilansu na cewar waannan rijista baya cikin hurumun dokar senso,

kuma abunda yke cikin hurumun dokar senso shine ita tana hulda ne da kungiyoyi kowacce kungiya zata kawowa senso ne adadin mutanan da suke dasu da sunayensu, sabida haka idan ma akasamu wani abu to gwamnati zata umarci kungiya ne data kawo mata wane wanda yake cikin wannan kungiya
to akan haka tsarin yake sabida haka duk wadanda suka ki zuwa suyi rijista da senso to akan wadannan dalilan suka ki duk wadan da kaga kuma sunbu gwamnati sunje sunyi to sabida su zauna lafiyane

saboda haka wannan kuma munzo munyi a junanmu sabida matsalar da muke ciki tayi yawa harkar cd ta mutu harkar sinima ta mutu harkar gidan tv ta mutu in kai film dinma sai dai kai asara sabida haka dole sai mun futo wannan rashin jin dadi da muka tsunci kanmu shiyasa muka futar da wannan matsaya da kanmu,

dama de wannan masana anta ta kannywood ta dade tana fuskantar matsaloli wadanda har yanzu an kasa shawo kansu

in Allah ya yarda zamu ci gaba da kawo muku tattaunawar da mukayi dashi,

Post a Comment

 
Top