Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa bata bakin ciki da sabbin mukaman da gwamnatin jihar Kaduna ta baiwa hambararren sarkin Kano,Muhammad Sanusi II.

 

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya baiwa Sarki Muhammad Sanusi II mukami a kwamitin kula da zuba jari na jihar. Ya kuma karawa sarkin mukamin shugaban jami’ar jihar ta Kaduna,KASU.

 

Da Punch ke tambayar hadimin gwamnan kan kafafen watsa labarai da Sadarwa, Salihu Tanko Yakasai ko me zasu ce kan wannan lamari?

 

Sai ya kada baki yace basu da matsala da mukaman da gwamnatin jihar Kaduna ta ba sarkin kuma basa bakin ciki da hakan.

 

Ya kara da cewa gwamnatin Kaduna na da hurumin yin hakan.



© hutudole

Post a Comment

 
Top