Rahotanni na kara bayyana kan irin zaman da Hambararren Sarkin Kano zai yi a garin Loko na jihar Nasarawa inda yake samun Mafaka.

 

Bayani  da Hutudole ya samu na cewa, Sarkin zai kasance cikin daurin talala a gidan da za’a ajiyeshi.

 

Sannan kuma ba za’a bari kowa ya kaimai ziyara ba.

 

Wannan magana ta fitone daga bakin hadimin gwamnan Kanon kan kafafen watsa labarai da Sadarwa  Salihu Tanko Yakasai.

 

Ya bayyana a jiya, Litinin cewa, Ga dukkan Alamu mutane da yawa basu san abinda ake nufi da tsige sarki ba, idan aka tsige Sarki yawanci ana kaishi can wani gurine dake da wahalar zuwa, a killaceshi kuma ba za’a bari a rika kaimai ziyara ba.

 

Mutumin dake cikin irin wannan hali zai ji ne da samun ‘yancin kanshi ba maganar zabe na gababa.

 

Yakasai yayi wannan maganane ta shafinshi na sada zumuntar Twitter kuma ga dukkan alamu yana baiwa masu ruruta cewa Sarkin Kano ya shiga siyasane martani.



© hutudole

Post a Comment

  1. Ya Kanata adene wannan irin mulkin gargajiyannan ,mufa yanxu munsamu yanci ,wannan abin da akayiwa sarki sanusi bashi a constitution na kasa

    ReplyDelete

 
Top