Hukumar kashe gobara tare da hukumar tsaro ta farin kaya wadda a kafi sani da Civil Defence, da kuma hukumar shige da fice Immigration CDFIB hukumar ta amince da daukan Sababun ma’aikata a shekarar da muke ciki ta 2020.

 

A cewar Jami’i maigana da yawun hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya, NIS, Sundaye James ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a babban birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a, inda yace kwamitin gudanarwa a karkashin jagorancin Ministan cikin gida Rauf Aregbesola ne ta amince da daukan aikin.

 

An ware kusan makonni hudu domin daukan aikin daga ranar da aka sanar a hukumance, don haka ake kira ga jama’a su yi amfani da wannan dama domin su nemi aikin nan.” Inji shi.

 

Bayan haka Sunday ya gargadi jama’a dasu kula wajan shiga yanar gizon da ba na hukumar ba da nufin neman aikin, inda ya bayyana sahihin adireshin yanar gizon hukumar kamar haka:

 

https://ift.tt/2q82qhN.

 

A karshe yayi kira da a kula wajan bin dokoki gun Neman aikin kuma ya Kara da cewa Neman aikin a hukumar kyauta ne.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top