Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya baiyana batun sauke tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi a matsayin ‘alheri’ da mara kyau ‘.

 

A cikin wata wasika, inda ya yi magana da Sanusi da cewa “Maigirma kuma dan’uwana,” ya kuma ce masa “ya ji labarin bakin ciki da albishir da kwamitin Majalisar zartarwa na gwamnatin jihar Kano ta yi”.

 

Obasanjo ya ce cire Sanusi abin bakin ciki ne domin bai cancanta ba, amma yana da kyau saboda tsohon Sarkin ya “biya farashin”. sai dai bayyi bayani dalla-dalla ba.

 

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da cire Sanusi a safiyar Litinin daga kan karagar mulki, lamarin da ya kawo karshen wata kyakkyawar alakar da ke tsakanin tsohon Sarkin da gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

 

A karshe tsohon shugaban kasar ya bayyana da cewa ” Addu’ata ita ce Allah ya ba ka ƙarfin zuciya da ƙarfin gwiwa don ci gaba da bin tafarkin da ka zaɓa don kanka don amfanin ƙasarmu da alumma,” in ji Obasanjo.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top