Tauraron me bayar da umarni na fina-finan Hausa kuma Jarumi, Falalu A. Dorayi ya bayyana ra’ayinsa kan sauke Sarki Muhammad Sanusi II daga sarauta.

 

A sakon da ya rubuta a shafinsa na sada zumunta Falalu yayi tuni da Imani da Kaddara.

 

Fafalu yayi rubutu kamar haka:

 

Babu wani abu da zai faru a doran duniya babu sanin Allah,
Tsakanin Alkairi da Akasin haka.

Tsakanin wanda aka cire da wanda aka dora dukkan su suna rayuwa ne akan Littafin Kaddara, a rubuce yake sai hakan ya kasance tare dasu.

Yana cikin tarbiyar Addini yadda da kaddara mai kyau da mara kyau, a kano kaddara 2 ce ta sauka, a bangare daya kukan bakin ciki a ke, a daya bangaren kuka farin ciki a ke. Kuma hakan zatai ta faruwa a rayuwar duk wanda ya kadaita Allah. Yau farin ciki gobe akasin haka.

Al’amarin rayuwar musulmi so ake ya kasance mai hakuri da fadin gaskiya domin Allah, hakan zai bashi kyakkyawan sakamako.

Idan har fadawa masu mulkin siyasa gaskiya ne yasa aka cire shi, to dama ita gaskiya haka take zuwa, bata bukatar ado amma mai fadinta ya shirya karbar Kalubale, wasu Idan suka fade ta ma duka suke ci, wasu kuwa fadin gaskiya ya kan janyo su rabu da rayuwarsu. mun gani a cikin Yan kananan shekarun da Allah ya bamu.

Idan kuma abubuwan da gwamnatin kano ta fitar sune hujjar ta, gwamnati na da hurumin hukunci. sai dai kuma tsaurin hukuncin da tayi kamar famawa mai gyambo ciwo ne, domin sarautar kano zata zama kamar rayuwar Yan siyasa duk gwamna zai zo da sarkin sa zai zo, idan ya tashi sauka su tafi tare. Allah ka kare kano da masarautarta.

Ni Falalu na fi yarda Yafi kama da hankali a fadawa mutum ko Jagora gaskiya a gaban sa da a koma gefe ana cin namansa.

Sannan Yafi kama da rashin hankali musulmi ya ringa farin ciki da fadawar wani Cikin matsala, mai kake dashi na tabbas daga gurin Allah da zai kasance a karshen rayuwarka?

Allah ya taimaki Sabon Sarki kano
Alhaji Aminu Ado Bayero
Allah bashi ikon riko da adalci.

Sarki Muhammadu Sunusi na ||
Da iyalansa Allah ya basu Dangana.

 

View this post on Instagram

S A R A U T A R K A N O Babu wani abu da zai faru a doran duniya babu sanin Allah, Tsakanin Alkairi da Akasin haka. Tsakanin wanda aka cire da wanda aka dora dukkan su suna rayuwa ne akan Littafin Kaddara, a rubuce yake sai hakan ya kasance tare dasu. Yana cikin tarbiyar Addini yadda da kaddara mai kyau da mara kyau, a kano kaddara 2 ce ta sauka, a bangare daya kukan bakin ciki a ke, a daya bangaren kuka farin ciki a ke. Kuma hakan zatai ta faruwa a rayuwar duk wanda ya kadaita Allah. Yau farin ciki gobe akasin haka. Al’amarin rayuwar musulmi so ake ya kasance mai hakuri da fadin gaskiya domin Allah, hakan zai bashi kyakkyawan sakamako. Idan har fadawa masu mulkin siyasa gaskiya ne yasa aka cire shi, to dama ita gaskiya haka take zuwa, bata bukatar ado amma mai fadinta ya shirya karbar Kalubale, wasu Idan suka fade ta ma duka suke ci, wasu kuwa fadin gaskiya ya kan janyo su rabu da rayuwarsu. mun gani a cikin Yan kananan shekarun da Allah ya bamu. Idan kuma abubuwan da gwamnatin kano ta fitar sune hujjar ta, gwamnati na da hurumin hukunci. sai dai kuma tsaurin hukuncin da tayi kamar famawa mai gyambo ciwo ne, domin sarautar kano zata zama kamar rayuwar Yan siyasa duk gwamna zai zo da sarkin sa zai zo, idan ya tashi sauka su tafi tare. Allah ka kare kano da masarautarta. Ni Falalu na fi yarda Yafi kama da hankali a fadawa mutum ko Jagora gaskiya a gaban sa da a koma gefe ana cin namansa. Sannan Yafi kama da rashin hankali musulmi ya ringa farin ciki da fadawar wani Cikin matsala, mai kake dashi na tabbas daga gurin Allah da zai kasance a karshen rayuwarka? Allah ya taimaki Sabon Sarki kano Alhaji Aminu Ado Bayero Allah bashi ikon riko da adalci. Sarki Muhammadu Sunusi na || Da iyalansa Allah ya basu Dangana. #FalaluADorayi #Baba

A post shared by F A L A L U A. D O R A Y I (@falalu_a_dorayi) on

 

 



© hutudole

Post a Comment

 
Top