Jagoran Kungiyoyin Matasan Arewa Murtala Abubakar ya bayyana cewa dole ne a zargi Shugaban Kasa Buhari saboda rashin sanya baki kan tsige Sarkin Kano Sunusi.

 

Ya kara da cewa abinda ya faru a Kano na tsige Sarkin Kano Sunusi abun takaici ne, kuma abune da zai shafi tattalin arzikin Jihar da kuma kawo dar dar ta fannin tsaro a jihar dama arewancin Najeri.

 

A cewar sa batun rikicin da ya kunno kai tsakanin Masarauta da Gwamnati batune da za a iya shawo kansa, tuntuni muddin akwai kyawun shugabanci da suke da kishin yankin Arewa.

 

Ya kuma bayyana cewa furucin da Shugaban kasa ya fada, lokacin da Gwamnan kano da Sarkin Bichi suka Kai masa ziyara akan cewa Bazai musu ka tsalan ba akan sha’aninsu ne, yasa Gwamnan Kano ya samu kaimin ai watar da abinda yake so.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top