Abdulrahman Pantami, dan Ministan Sadarwa, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya yi kira da a kara tallafawa yan gudun Hijira wajan samar musu da Ilimi da kuma kula da lafiyarsu.
Pantami, wanda ya yi jawabi a bikin tunawa da ranar yara ta duniya, a cewar sa yawaitar rashin ilimi dake addabar wani bangare a Arewa cin Najeriya na samuwa ne sakamakon Masu tada kayar baya, Na yan Boko Haram.
Ya ce ilimi abune mai muhimminci wanda a yanzu yake a cikin wani hali, ya zama dole da a magance ta’addanci a Arewa.
Pantami ya koka da halin rashin ababen more rayuwa a wasu sansanonin ‘yan gudun hijira inda ya yi kira ga ma’aikatar kiwon lafiya ta tarayya da ta jihohi da su taimaka wajen magance matsalar.
A karshe ya godewa gwamnan Jihar Barno bisa kokarin da yake.
© Abubakar Saddiq
Post a Comment