An daga wasan Premier League Wanda za a buga yau, laraba a filin wasan Etihad tsakanin Arsenal da Manchester City saboda barazanar cutar coronavirus-Covid-19.

 

Hukumar gasar Premier League tace an samu labarin cewa mai horas da kungiyar olympiakos, Evangelos Marinakis na dauke da kwayar cutar coronavirus-COVID-19.

 

Arsenal ta tabbatar da cewa akwai yan wasanta da dama da suka je wajen Marinakis bayan sun buga wasan su na zakarun nahiyar turai wato (Europa league ) kuma wa’yan nan yan wasan yanzu haka sun kebance  kansu.

 

Kungiyar ta kuma cewa hukumar lafiya tace a shawarce wasan da za’a buga yau tsakanin Arsenal da Man city ya kamata a daga shi saboda a samu isashan lokaci a shawo kan matsalar.

 

Saboda haka hukumar Premier League ta aminta cewa wasan da zai gabata yau da daddare za’a sake shirya mai wani lokacin.



© hutudole

Post a Comment

 
Top