Shugaban rukunin kamfanin Albarkatun man fetur na kasa,NNPC Mele Kolo Kyari ya bukaci ‘yan Najeriya da su shiryawa sabon matsin tattalin arziki dake tunkarar kasar.

 

Kyari yayi wannan maganane a wajan wani taro da yayi da babban bankin Najeriya, CBN.

 

Yana magane saboda faduwar da farashin danyen man fetur yayi kasa wanwar wanda rabon da aga haka tun shekarar 1999. Hakan ya samo Asaline daga fargabar cutar Coronavirus/COVID-19 da ta tilastawa wasu kasashen rufe iyakokinsu da kuma yanke hulda da wasu kasashe hadi da yawan da man yayi.

 

Akwai dai jiragen ruwan dakon mai dake tangaririya akan teku babu gurin zuwa saboda ba inda ke da bukatar man.

 

Kyari yace an saka tsammanin farashin mai na tsaya akan dala 60 kowace ganga amma yanzu dala 30 yake kuma watakila ma ya kara faduwa kasa. Yace dan haka dolene sai an shiga matsin tattalin arziki lura da cewa tattalin arzikin Najeriyar ya ta’allakane akan Manfetur din.

 

Ya kara da cewa koda kuwa ace Farashin ya sake tashe to akalla sai ya kai wani lokaci kamin a dawo daidai dan haka  yan Najeriya su shiryawa matsin tattalin arziki na akalla watsanni 3.



© hutudole

Post a Comment

 
Top