Wasu gun-gun ‘yan mata sun cafke wani matashi da suke zargi da satar lefen ‘yar uwar su a unguwar Sheka Rigar Kuka dake nan Kano.

Wasu daga cikin ‘yan matan da sukayi rubdugu wajen cafke matashin sun shaidawa Freedom Radio cewa matashin ya kutsa cikin gidan su, tare da satar atamfofi da leshi cikin akwatun kayan lefe.

 

Shi ma a nasa bangaren matashin da aka cafke ya shaidawa Freedom Radio cewa babu shakka ‘yan matan sun ci zarafin sa, sun kuma keta masa haddi wajen yi masa duka da tara masa jama’a, don kawai ya saci kayan lefen su.

 

Yunusa Sulaiman Sheka shi ne kwamandan jami’an sintiri na yankin unguwar Sheka ya shaidawa wakilin mu Yusuf Ali Abdallah cewa yanzu haka matashin yana hannunsu inda suke shirin mika shi ga ‘yan sanda.

Freedomradio



© hutudole

Post a Comment

 
Top