Paris Saint Germain (PSG) a ranar Talata ta yiwa tauraron matashin dan wasanta, Kylian MbappĂ© gwaji don ganin ko yana da cutar COVID-19 tun bayan da dan wasan ya kauracewa Atisaye har na tsawan kwana biyu (Litinin da Talata) inda aka rawaito dan wasan na fama da ciwo a Makogaro , in ji rahoton jaridar Faransa, L’ Lquipe.
A sakamakon gwajin da kawararrun likitocin kungiyar (PSG) suka sanar ya tabbatar da dan wasan bai kamu da cutar COVID-19 ba.
Ana tunanin Mbappe shine dan kwallon kafa na farko da aka fara masa gwajin cutar COVID-19, wanda ya bazu ko’ina cikin Duniya a cikin ‘yan makonnin nan.
Har yanzu ba a tabbatar da matsayin Mbappe ba game da wasan da kungiyarsa zata buga da Borussia Dortmund na gasar Champions League zagaye na 2 na kungiyoyi 16 da suka rage a gasar a yau. A zagaye na farko Dortmun ta ci PSG 2-1.
© Abubakar Saddiq
Post a Comment