Watarana Wani mutum yazo wajen Maulana shehu ibrahim inyass yace

Shehu ni sharifi ne jikan ANNABI S.A.W na zo ne kabani hadiyya ne

Sai Shehu yayimasa hadiyya mai nauyi har da riguna na alfarma

Wannan mutum ya shiga kasuwa da niyyar sayar da rigunan da shehu ya bashi

Sai yake bada labari yake cewa Shehu baida wayau kawai dan nace mashi ni sharifine kalli irin abunda yabani

Labari yazo wurin shehu Nan take Sai shehu yace a nemo mutumin nan bayan an zo dashi

Sai Shehu ya sake dauko kudi da kaya wanda yafi nada yabashi

Shehu yace nagode wa Allah tunda mutane sun gane idan suka zomin da Annabi S.A.W zan yimusu dukkan abinda sukeso

Allah kabarmu da shehu R.T.A

Post a Comment

 
Top