Daya daga cikin dalilan da ya sa aka kori Muhammad Sanusi na II a matsayin Sarkin Kano shi ne yawan sukar da ya ke yi wa gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje, in ji daya daga cikin Mashawarci na musamman ga gwamna, Salihu Yakasai.

 

Yakasai, wanda ya bayyana hakan a shirin Tashar Talabijin na Channels ranar Talata, ya ce babu wani mulki da zai iya juriya ga suka bainar jama’a.

 

Ya ce Sanusi, wanda yake da saukin saduwa da gwamna Ganduje, yakamata ya rika tattaunawan da suka shafi jihar a tsakanin su, maimakon sukar sa a bainar jama’a.

 

Mai magana da yawun gwamnan ya ce, “Sarkin yana da damar zuwa wurin gwamnan a kwani lokaci, kuma zai iya ba shi shawara idan yana so amma abin takaici, ya zabi mimbari da manyan taruka a matsayin hanya daya tilo da zai rika baiwa gwamnati shawara, wacce ba ta dace ba.”

 

Yakasai ya ce, alal misali, mai martaba sarki ya soki shirin gwamnatin Kano na raya biranai a bainar jama’a, alhali yana damar ganin gwamnan kai tsaye.

 

Ya ce, “Tun lokacin da gwamna Ganduje ya kirkiro sabbin masarautun jihar Kano, za ku iya kirga adadin muhimman tarurruka da gwamnatin jihar ta shirya ciki har da halartar kasa da kasa wanda aka gayyaci mai martaba sarki kuma bai taba halarta ba.”

 

Yakasai ya yi zargin cewa har ma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, har sau 4 ya bukaci sarki Sanusi da yayi masa Karin bayani kan wasu zarge-zarge, inda ya kara da cewa Ganduje ya cancanci yabo saboda sassaucinsa.

RFIhausa.



© hutudole

Post a Comment

 
Top