Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayi gargadin cewar barazanar da kasar ke fuskanta daga annobar murar Coronavirus somin tabi ne kawai.

 

Shugaba Macron yayi gargadin ne bayan da ma’aikatar lafiyar kasar ta bada rahoton karuwar wadanda annobar ta halaka zuwa mutane 30, yayinda wasu dubu 1 da 606 suka kamu.

 

Yanzu haka dai Faransa ce kasa ta 2 bayan Italiya da annobar murar ta corona tafi shafa a nahiyar Turai, abinda ya sanya gwamnatin kasar tsaurara matakan yakar cutar.

 

A nahiyar Turan a talatar nan Kasar Spain ta yi shelar dakatar da zirga-zirgar jiragen sama tsakaninta da Italiya na tsawon makwanni 2 saboda annobar coronavirus, bayanda adadin wadanda annobar ta shafa a kasar ya kai dubu 1 da 622 tare da kashe wasu 35.

 

Matakin na Spain ya zo ne bayan da gwamnatin Italiya ta dauki matakin killace ilahirin al’ummar kasar, ta hanyar basu umarnin zama a gida bayanda annobar ta Corona kashe mutane 453 da kama wasu sama da dubu 9.

 

Italiya ce kasuwa ta uku mafi girma ga kamfanonin jiragen Spain, la’akari da cewa a 2019 kididdiga ta nuna cewar jimillar fasinjoji miliyan 16 ne suka yi zirga zirga tsakanin kasashen biyu da adadin jirage dubu 106 a shekarar guda kadai.

 

A Jamhuriyar Czech kuma, Yau talata gwamnati ta bada umarnin rufe baki dayan makarantun kasar, yayinda Slovakia kuma ta rufe mujami’un kasar, ita kuma Poland ta soke dukkanin tarukan jama’a domin dakile yaduwar annobar coronavirus dake dada karfi a yankin tsakiyar Turai.



© hutudole

Post a Comment

 
Top