Alamomi na nuna cewa, a ranar Alhamis Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya ziyarci garin Awe da ke jihar Nasarawa don ziyartar sabon matsugunin Muhammadu Sanusi II da aka tube daga sarautar Kano.

 

Gwamnan ya bar jihar ne da safiyar Alhamis don ziyartar Sanusi II.

 

Wakilinmu, ya tuntubi Mai taimakawa Gwamnan Kaduna a kan watsa labarai Ibrahim Musa, amma bai samu lambar wayar salularsa ba don jin karin bayani.

 

Rahoton bai tabbatar da cewa, Gwamna El-Rufai ya dawo da jihar ba.

 

Idan ba a manta a cikin awa 24 da tube Sarkin Gwamnan ya bai wa Sanusi II mukami.



© hutudole

Post a Comment

 
Top