Kawo yanzu, adadin mutanen da cutar Coronavirus ta kashe ya zarta dubu 5 a sassan duniya, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ya tattaro daga alkaluman da mahukunta suka fitar. Wannan na zuwa ne a yayin da kasar Iran ta sanar da sabbin mutane 85 da cutar aika lahira a yau Juma’a, yayin da kasashen Turai da dama suka rufe makarantu don dakile yaduwar wannan annubar.

 

Jumullar mutane dubu 3 da 176 sun mutu a kwaryar China kadai, sai kuma dubu 1 da 16 da suka mutu a Italiya, yayin da cutar ta hallaka 514 a Iran.

 

Wadannan kasashe uku ne ke kan gaba wajen samun asarar rayuka a duniya a sanadiyar Coronavirus.

 

Iran ta ce, a cikin sa’o’i 24 da suka shude, Coronavirus ta kashe mata mutane 85, abin da ya sa alkaluman mamata a kasar suka kai 514 kamar yada ma’aiktar kiwon lafiyar kasar ta sanar.

 

Yanzu haka jumullar Iraniyawa dubu 11 da 364 aka tabbatar sun harbu da cutar mai sarke hanyar numfashi.

 

Da dama daga cikin ‘yan siyasar Iran sun kamu da cutar.

 

 

Ita kuwa gwamnatin Faransa ta sanar da rufe cibiyoyin karatu har tsawon makwanni biyu a wani mataki na dakile yaduwar wannan annuba a kasar, yayin da a gefe guda, gwamnatin ta Faransa a haramta taron mutanen da adadinsu ya zarce 100 sabanin 1,000 da ta ayyana a baya.

 

Kasashe irinsu Jamus da Switzerland da Potugal da Belgium har ma da Ireland duk sun dauki matakan rufe makarantunsu.

 

Kawo yanzu wannan cuta ta harbi sama da mutane 134 a kasashen duniya 121 da ta bulla.



© hutudole

Post a Comment

 
Top