Tsohon sarkin Kano,Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa daga fadar gwamnatin tarayyane aka bayar da umarnin tsareshi.
Sanusi ya kara da cewa bayan da aka saukeshi a matsayin sarkin Kano, Wani abokinshi ya aikamai da jirgi dan a kwasheshi shi da iyalinshi zuwa Legas.
Yace da kwamishinan ‘yansandan Kano ya je masa sai ya bijiro da bukatar tafiya Legas. Yace amma sai kwamishinan ya gaya mai cewa ba umarnin da aka bashi ba kenan daga Abuja.
Yace an ce maine ya kaishi babban birnin tarayya, Abuja.
Wanna bayani na kunshene cikin korafin da Sarkin ya shigar gaban babbar kotun gwamnatin tarayya dake Abuja.
Ya kara da cewa saukeshi da aka yi daga mukaminshi ba abi ka’ida ba dan ba’a bashi damar kare kanshi ba, saidai yace ba zai kalubalanci saukeshin ba.
Ya kara da cewa yana neman diyyar Miliyan 50 daga wadanda suka mai cin zarafin tsareshi da hanashi ganawa da iyalanshi da abokai.
Ya dora alhakin tsareshin da aka yi kan Atoni janar na Shugaban kasa da kuma Atoni janar na Gwamnatin Kano.
© hutudole
Post a Comment