Yan tawagar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da sauran ma’aikatan kungiyar sun kebance kansu da kansu a yayin da suke da wasa tasakanin suda Aston villa saboda fargabar Coronavirus/COVID-19.
Alamun cutar Covid-19 sun bayyana akan Hudson-Odoi ranar Litinin wanda hakan yasa aka kebance shi da sauran yan wasan, An samu sakamakon gwajin da aka yimai ranar alhamis dadaddare wanda hakan ya tabbatar da cewa yana dauke da cutar Coronavirus/COVID-19 kuma shine dan wasan Premier League na farko daya fara kamuwa da cutar.
Da safiyar juma’a ne kulob din Chelsea suka ce gaba daya yan wasan su da kocinan su da kuma sauran ma’aikatan su sun killace kansu da kansu.
Kuma sauran ma’aikatan Chelsea da suka yi mu’amala da dan wasan zasu bi sharuddan cutar da hukumar lafiya da kuma gwamnati suka tsara na killace kai.
Ana sa ran cewa sauran ma’aikatan Chelsea da basuyi mu’amala da dan wasan ba zasu dawo kan aiki bada dadewa ba.
Yan kungiyar sunce duk da cewa an samu dan wasan mai shekaru 19 da cutar, suna sa ran zai dawo kan aiki bada dadewa ba saboda dan wasan England yana da kokari sosai.
Hukumar Premier League yi taro a yau jJuma’a domin su san irin hukuncin daya kamata a dauka gami da cutar Covid-19 kamar yadda aka samu labari cewa kocin Arsenal Mikel Arteta yana dauke da cutar.
© hutudole
Post a Comment