Zababben gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya godewa mutanen Jihar Kaduna bisa sake Zaben sa da suka yi a Karo ta biyu domin ya mulki Jihar.

El-Rufai ya bayyana haka ne a jawabin godiya da yayi wa mutanen Jihar Kaduna ranar Litinin.

” Kun nuna mini halasci a Kaduna, tabbas zan muku halasci domin kuwa zan tabbata na kwarara wa duk dan Jihar Kaduna romon dimokradiyya har gida.

” Kun bani damar zabar mace ta farko a matsayin mataimakiyar gwamna a Kaduna. Da ni da Hadiza Sabuwa Balarabe zamu tabbata ba kuyi da na sani ba a zaben da kuka yi.

” A wannan karon mun hada kai mun yi wa wasu da ke ganin su shafaffu da mai ne sannan ba za a iya taka su ba duk da yin yadda suka ga dama a Jihar mun yi musu murabus a siyasa.

” Bayan haka ina so in yi amfani da wannan Dana domin in jinjina was mutanen karamar Hukumar Zariya bisa ruwar kuri’u da suka yi wa shugaba Muhammadu Buhari da babu wata yanki a Jihar Kaduna da ta bashi irin wannan kuri’u.

” Anyi amfani da sauye-sauyen da muka yi don saita Jihar kan hanya madaidaiciya wajen fatattakar baragurbin malamai, da ma’aikatan da Basu cancanta ba da suka cika ma’aikatun mu da kananan hukumomi da gyara Jihar mu don a rudi talakawa amma hakan baiyi tasiri ba domin su talakawa sun sani don su muke yi ba don wadannan da suka zame wa Jihar kashin kifi ba.

El-Rufai ya karkare da cewa gwamnati zata ci gaba da ayyukan ci gaba a Jihar Kaduna domin mutanen Jihar.

Premiumtimeshausa.

Post a Comment

 
Top