A wata takar da da ta fito daga gidan Kashim Ibrahim, Gwamna Nasir El-Rufai ya amince da kafa shugabannin cibiyar KADIPA din.
An kafa cibiyar ne a 2015 kuma tana kan gaba ne wajen habaka kasuwancin jihar tare da saukakawa kasuwanci a jihar Kaduna. Bankin Duniya kuwa ya kalla cibiyar a matsayin ta farko a fannin kasuwanci a Najeriya.
Sanarwar da mai bawa gwamna shawara a fanin watsa labarai, Muyiwa Adekeye ya aike wa Premium Times a ranar Talata ta ce, “Malam Nasir El-Rufai ya amince da zaben mai martaba, Muhammadu Sanusi II zuwa shugabancin KADIPA. Cibiyar ta samu shugabancin mataimakiyar gwamnan tare da sauran jiga-jigai a gwamnatin jihar."
Yanzu-yanzu: Bayan sauke shi daga mulki, gwamnatin Kaduna ta bawa Sanusi II babban mukami
“Gwamna Nasir El-Rufai na fatan cin gajiyar gogewa da kwarewar Sanusi wanda ya gina ginshiki a fannin tattalin arziki a duniya kafin zamansa sarki. Malam Nasir El-Rufai ya ce jihar Kaduna na tsananin farin ciki da alfaharin samun aikin mutum kamarsa," in ji shi
Ya cigaba da cewa, “Ya kara da jaddada cewa babu shakka sabbin shugabannin KADIPA din zasu kara habaka cibiyar ta yadda zata jawo hankalin masu zuba hannayen jari. Ya kara da cewa mambobin da aka zabo an tsamosu ne tare da kiyayewa."
Ga jerin sunayen shugabannin KADIPA din kamar haka:
1. Mataimakiyar gwamna, Dr. Hadiza Balarabe Chairman
2. Mai martaba, Muhammadu Sanusi II Vice-Chairman
3. Balarabe Abbas Lawal, Sakataren gwamnatin
jihar
4. Bariatu Y. Mohammed, Shugaban ma’aikata
5. Jimi Lawal, Babban mai bada shawara
6. Aisha Dikko, Kwamishinan shari’ar jihar Kaduna
7. Idris Nyam, Kwamishinan kasuwanci, kirkirre-kirkire da fasaha
8. Fausat Ibikunle, Kwamishinan gidaje
9. Thomas Gyang, Kwamsihinan tsari da tattali
10. Farida Dankaka, KACCIMA
11. Amal Hassan, Bangaren ma’aikatu maus zaman kansu
12. Hafiz Bayero, shugaban hukumar habaka kasuwannin jihar Kaduna
13. Altine Jibrin, Babban daraktan KADGIS
14. Umma Aboki, Sakataren, KADIPA
Post a Comment