Sabon labari da dumi-duminshi dake fitowa daga fadar shugaban kasa, Muhammadu Buhari shine,shugaban kasar ne ya baiwa Gwamnan Kaduna,Malam Nasiru Ahmad El-Rufai Umarnin baiwa Hambararren sarkin Kano mukaman da ya bashi.

 

Gwamnan Kaduna dai bayan awanni 24 da sauke Sarki Muhammad Sanusi II ya sanar da cewa ya baiwa Sarkin Mataimakin shugaban kwamitin zuba jari na jihar Kaduna.

 

Jim kadan kuma sai gashi ya karawa Sarki Sanusi mukamin Shugaban jami’ar Jihar Kaduna.

 

A sakon da ya fitar ta shafinshi na Twitter,hadimin shugaban kasa ta fannin Sabbin kafafen Sadarwa, Bashir Ahmad ya bayyana cewa har yanzu bai ji wani ya yabawa shugaban kasa,Muhammadu Buhari ba kan mukaman da yasa Gwamnan Gaduna ya baiwa Sarki Sanusi ba.

 

Ya kara da cewa Duka gidajen jaridu su dauki wannan labari su yadashi.

 



© hutudole

Post a Comment

 
Top