Sau da yawa mutum baya sanin amfanin ‘yancin shi har sai ya kubuce mishi

- Wasu mata masu matukar bukatar jima’i da ke gidan yarin Malindi Kilifi a kasar Kenya sun roki gwamnatin kasar

- Matan sun bayyana a matse ne kuma cikin takura yayin da suka bayyana wannan bukatar ga gwamnatin kasar

Wasu mata masu matukar bukatar jima’i da ke gidan yarin Malindi Kilifi a kasar Kenya sun roki gwamnatin kasar da ta saka sabuwar doka da za ta bar su jin dadin junansu da mazansu yayin da suka kai musu ziyara, jaridar pulse.ng ta ruwaito.

Matan sun bayyana a matse ne kuma cikin takura yayin da suka bayyana wannan bukatar ga gwamnatin kasar.

Daya daga cikin ‘yan gidan yarin, Sofia Swaleh, wacce ke fuskantar hukuncin daurin rai da rai tayi magana a madadin ‘yan uwanta mata na gidan.

Kamar yadda ta ce, lokacin da ake ba mazansu na ganinsu yayin da aka kawo musu ziyara yayi kadan. Hakazalika basu samun damar kwanciya da mazansu din.

Gwamnati ta hannun shugabannin gidan gyaran halin ya kamata su kirkiro dokar da za ta bar matan da ke gidan yarin samun damar kwanciya da mazansu na aure bayan sun kawo musu ziyara,” Swaleh tace.

A halin yanzu, matukar aka yankewa mutum hukunci na zaman gidan gyaran hali, da yawa daga cikin hakkokinsa na dan kasa kan bi ruwa.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu irin wannan korafin a 2014 amma gwamnatin kasar tayi watsi dasu tare da cewa bata shirya musu ba.

©Naij

Post a Comment

 
Top