Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Kebbi a ranar Alhamis, don bude bukin al’adun gargajiya da kamun Kifi a Argungu.

 

A lokacin da shugaban yake zagayawa don ganin yadda ake baje kolin shinkafa da kuma daukar hotuna da manoma, sai wani matashi da ke tsakanin al’umma ya kutsa kai ya nifi in da shugaban ya ke da karfin gaske.

 

Kamar yadda duniya ta sani, jami’an tsaro basu bashi damar isa wajen shugaban ba, nan take aka hana yaron kusantar Shugaban.

 

Lamarin da ya janyo aka dinga yada rahotanni kan shafukan sada zumunta masu cewa an kai wa shugaban hari.

 

Amma tuni mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar da sanarwa kan abinda ya faru.

“Mutane marasa fatan alheri a kullun suna neman sauya zahirin abu idan ya faru domin a bashi wata fahimta ta daban,” a cewarsa.

 

“Basu san hakan bata da wani amfani garesu ba, kuma dole kasa ta ci gaba.”

 

Kafin nan ma, mai bai wa shugaban shawara ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa “matashin masoyin Buhari ne, kuma ya nufi wurinsa ne domin ya bashi hannu.”

 

Har yanzu dai ana ta ce-ce ku-ce kan gaskiyar abinda ya faru, inda mutane da dama ke da ra’ayoyi mabambanta.

 

Wannan dai shi ne karo na farko da aka gudanar da bukin na al’adar gargajiya da kamun kifi cikin cikin shekaru goma saboda matsalolin tsaro.



© hutudole

Post a Comment

 
Top