Dan wasan baya Daniele Rugani shine dan wasan Serie A daya fara kamuwa da cutar Covid-19 kuma ya kasance daya daga cikin yan kulob din juventus  wanda suka hada dakin canja kaya daya da sauran yan wasan bayan sun yi nasarar wasan su da inter Milan.
Yan kungiyar sun ce bayan jiya an tabbatar da cewa Rugani yana dauke da cutar Covid-19, Hakan yasa yan kungiyar guda 121 suka taimaka suka killace kansu da kansu kamar yadda doka ta tanadar kuma sun hada da yan wasan su da ma’aikatan su da da jami’an tsaro masu rakiya.
Duk da cewa an ruwaito abokin aikin Rugani ya kamu da cutar coronavirus wato Dybala kasar Argentina ta karyata cewa bai kamu da cutar ba. Dan wasan a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa inaso in tabbatar wa mutane cewa lafiyata kalau nagode da sakonnin ku da fatan kuma kuna cikin koshin lafiya.
Cristiano Ronaldo bazai koma kasar italia ba saboda cutar tana cigaba da yaduwa a yankin.ayayin da yaje Madeira don ziyartar mahaifiyar shi saboda batada lafiya. Dan wasan juve pjanic ya saka wani hoto a Instagram,ayayin da Ronaldo da Rugani da sauran yan wasan suke murnar nasarar wasan su da inter Milan.
An soke gaba daya wasannin Italia harda wasan champions lig na juve da Lyon. Rugani ya zamo fitaccen dan wasa na biyu daya fara kamuwa da cutar. Kuma yace yana tabbatar wa masu shakka akan shi cewa lafiya shi kalau, kuma yana rokon mutane da su bi dokin cutar saboda cutar Bata nuna banbanci.


© hutudole

Post a Comment

 
Top