Coronavirus: Gwamnatin tarayya ta yi kashedin hana musayar hannu, da rungume rungumen juna.

 

A sakamakon coronavirus, Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya gargadi ‘yan Najeriya a kan musayar hannu da rungumar juna. Ya yi wannan gargadin ne jiya a yayin wani taron da ya gudana a wata cibiya dake Abuja.

 

Karku sake yin musayar hannu, ko rungumar junan Ku, sai ga Iyalan ku, kuyi nesa da kowa tsawan taku uku a duk lokacin da kuka hadu da wani, Inji ministan.

 

Ministan ya shawarci ‘yan Najeriya su yi gaisuwa ta hanyar durkusawa da taba zuciyar su.

 

A karshe yayi kira da yan Najeriya su cigaba da kula, sakamakon cutar corona ta zama cutar da ya kamata a maida hankali dan magance ta cikin gaggawa.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top