Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi kira ga ‘yan Najeriya, musamman musulmai, da su yi addu’a da gaske don Gwamnatin Tarayya ta shawo kan matsalolin rashin tsaro da kasar ke fuskanta.

 

El-Rufai ya kuma ce: “Allah ya bai wa shuwagabannin mu hikima don ganin yadda za su tabbatar da kasar ta cigaba.

 

Gwamnan, wanda ya yi magana a Abuja a yayin bikin cikar shekaru 25 na NASFAT tare da taken: ‘Ilimi a matsayin wani yanki na gina al’umma mafi inganci’, ya koka da cewa ya kamata Musulmai su rungumi kyawawan dabi’u komai halin da kasar ke ciki.

 

Don haka El-Rufai ya bukaci sarakunan gargajiya, na addini, dattawa, matasa da shugabannin siyasa su yi aiki tare don samun kyakkyawan shugabanci.

 

Ya bukaci dukkan ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da akidarsu ta addini ba, da su yi addu’ar zaman lafiya da daidaito a kasar.

 

Gwamnan, wanda ya samu wakilcin mai gudanarwa na ofishin addinai na jihar Kaduna, Alhaji Tahir Baba Ibrahim.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top