Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta fara tuntubar masu ruwa da tsaki a niyyarta ta rage farashin litar man fetur sakamakon karyewar darajar man fetur a kasuwar duniya kamar yadda Legit ta ruwaito.

 

Karamin ministan harkokin man fetur na kasa, Mista Timipre Sylva, ne ya bayyana hakan ranar Juma’a a Abuja.

 

Sylva, wanda ya jagoranci wani kwamiti na musamman da ya kafa, ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala ganawa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa, Villa.

 

Ministan ya kafa kwamitin ne domin ya yi duba, nazari tare da bayar da shawarwai a kan tasirin bullar ‘Corona Virus’ a kan tattalin arzikin Najeriya.

 

Sylva, tsohon gwamnan jihar Bayelsa a jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa har yanzu ba a tsayar da wata shawara a kan sabon farashin da za a mayar da litar man fetur ba, tare da bayyana cewa an fara tuntuba ne kawai.

 

“Tuntuba muke yi har yanzu, mu na kuma cigaba da bibiyar abubuwan da ke faruwa. Ana saka farashin litar man fetur ne bisa la’akari da farashin danyen man fetur.

 

“Ku cigaba da hakuri, za mu waiwaye ku,” a cewar ministan.

 

Farashin danyen man fetur ya fara fadu wa a kasuwar duniya tun watan Janairu bayan shugaba Buhari ya rattaba hannu a kan kasafin kudin kasa na shekarar 2020 a watan Disamba, 2019.



© hutudole

Post a Comment

 
Top