Babbar kotun gwamnatin tarayya dake da zamanta a babban birnin tarayya, Abuja ta bayar da umarnin sakin Sarki Sanusi II da ake mai daurin talala a garin Awe na jihar Nasarawa bayan saukeshi daga sarautar Kano.

 

Mai shari’a, Anwuli Chikere ne ya bada wannan umarni bayan da lauyan Sarkin,Lateef Fagbemi(SAN) ya shigar da kara yana kalubalantar tsarowat da akewa Sarkin.

 

Alkalin ya kuma bada umarnin baiwa wanda ake kara wannan hukunci da yayi.

 

Wanda ake kara dai sune Shugaban ‘yansanda,Muhammad Adamu, shugaban hukumar ‘yansandan farin kaya,DSS, Yusuf Bichi, me baiwa gwamnan jihar Kano Shawara kan Shari’a, Ibrahim Mukhtar da me baiwa Shugaban kasa shawara kan shari’a, Abubakar Malami.

 

Alkalin ya tsayar da ranar 26 ga watan Mayu dan ci gaba da sauraren karar.



© hutudole

Post a Comment

 
Top