Majalisar dattijai, a ranar Alhamis, ta zartar da karatu na biyu, akan daftarin sauye sauye na kundin tsarin mulki wanda ya tanadi mai Babbar Difuloma shine matsakaicin matakin da kowanne dan kasa zai iya amfani dashi dan tsayawa takarar shugabancin kasa a Najeriya ko Gwamnonin Jihohi.

 

Kudirin wanda memba na Jam’iyyar PDP daga jihar Filato, Sanata Isfifanus Gyang, ya gabatar, gudirin kuma ya tanadi mai Babbar Difulama na a matsayin matakin majalisar dokoki na tarayya dana Jihohi.

 

Haka zalika Kudirin ya nemi sauya kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya don samar da sauye sauyen sashe na 65 (2) (a), da 131 (d).

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya gabatar da kudirin ga Kwamitin Binciken Kundin Tsarin Mulki bayan da sanatocin suka gabatar da kudurin dokar karatu na biyu.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top