Tun bayan tsige sarkin da Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi, bisa rashin yiwa gwamnati biyayya da tsohon Sarkin ba yayi a cewar Gwamnatin Kano, biyo bayan hakan ke da wuya, sai aka jiyo Gwamnan Kaduna Nasiru El Rufa’i ya gwan-gwaje tsohon Sarkin da mukamai inda aka nada tsohon sarkin a matsayin shugaban gudanarwa na jami’ar jihar Kaduna (KASU).

An kuma nada Sanusi a matsayin mamba na hukumar inganta saka hannun jari na jihar ta Kaduna wato (KADIPA).

 

Rahotanni sun bayyana cewa Sanusi ya sanar da amincewa da karbar mukamin ne cikin wata sanarwa mai dauke da saka hannun hadimin Gwamna El-Rufai, Muyiwa Adekeye a ranar Laraba 11 ga watan Maris.

 

Bayan haka Gwamnan ya mika godiyarsa ga tsohon sarkin saboda ci gaba da bayar da goyon bayansa domin ganin jihar ta Kaduna ta cimma burinta.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top