Sabon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya zubar da hawaye bayan da ya samu wasikar nada shi daga hannun Ganduje.

 

Mai martaba Sarkin, wanda ya samu wasikar aiki daga gwamna Ganduje, ya fashe da kuka yayin da yake tuno yadda mahaifinsa, marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ya yi musu wa’azi game da juriya, hakuri da saukin kai.

 

Sarkin ya yabawa Ganduje bisa ga ayyukan al’khairi da ya ke bijirowa al’ummar Jihar kano, bada ilimi kyauta kuma dole, da hana bara a fadin Jihar gaba daya.

 

Da yake magana yayin taron, Gwamna Ganduje ya ce Kano ta kafa tarihi bayan an nada ‘yan uwan ​​biyu Sarakuna kuma tare sun karbi wasikunsu cikin farin ciki.

 

Babu wani lokaci da na ga jama’ar Kano suna murna da juna ba tare da rikice-rikice ba, babu nuna wariya, wannan abun farin ciki ne ga Jama’ar Kano, inji shi.

 

Ganduje ya kara da cewa an samu cikaken gyare-gyare a tsarin masarautar, tare da cigaban da aka samu kwanan nan



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top