Rundunar kasashen yankin tafkin Chadi ta ce ta hallaka daya daga cikin jagoran yan ta’addan yankin mai suna mallam Bakura.
Kakakin rundunar, kanar Timothy Antiga ya ce rundunar wacce ta kai farmaki tare da taimakon jiragen yakin sojojin saman Najeriya da Nijar da rundunonin mayakan Artillery, sun kai wani gagarumin farmaki a maboyar jagoran ‘yan ta’addan Mallam Bakura da ma sauran mukarrabansa a wani sarkakiyar bishiyoyi masu duhun gaske.
Wannan farmaki dai da aka tsara shi a tsanaki ya sami nasarar rugurguza baki dayan wannan maboya.
Babban kwamandan rundunar kasashen tafkin Chadin, manjo janar Ibrahim Manu Yusuf ya shaida wa muryar Amurka cewa ba zai so yayi dogon bayani ba kan wannan gagarumar nasara da aka samu, amma dai sun samu cimma burinsu ne da taimakon dakarun kasashen yankin da ma sauran jama’ar gari.
Mallam Bakura dai daya daga cikin jagororin ISWAP ne kafin daga bisani ya balle a shekara ta 2018 bayan da ya sami mummunan sabani da Abu Mossad Albarnawee.
A halin yanzu dai shi ne jagora a kungiyarsa da ke da tasiri a kudancin kasar Nijar da ma wasu tsibirai a tafkin chadi.
Masanin tsaro Dr. Kabiru Adamu ya ce girman aika aikar Bangaren Mallam Bakura akan iyakokin kasashen tafkin chadi ya zarce na bangarorin ISWAP da na Boko Haram.
An dai yi imanin shi ke addabar sassan kasar Nijar da Jihar Borno sannan yana da hanu dumu dumu wajen kai hare hare ga sojoji da fararen hula da satar mutane dan neman kudin fansa da kuma sauran nau’o’in ta’addanci a yankunan.
© hutudole
Post a Comment