Yan kungiyar Juventus sun cigaba da horo duk da cewa cutar Covid-19  tana cigaba da yaduwa amma dan wasan gaba maishekaru 35,  Cristiano Ronaldo ya tsaya a Madeira, mahaifarsa.

 

Tauraron juventus din yana zama a Madeira saboda kauce wa coronavirus kuma dama an dakatar da gasar Serie A.
Italy tafi kowace kasar turai kamuwa  da cutar Covid-19, Wanda a kalla kimamin mutane guda 12,462 ke dauke da cutar kuma ta dauke rayuwar mutane 827.
Firayam minista, Giuseppe Conte ya sanar cewa an dakatar da Serie A saboda yaduwar cutar coronavirus,Wanda hakan dole yasa aka daga manyan wasannin Italy makonnin dasuka gabata.

 

An dakatar da taron jama’a kuma gwamnatin ta hana dukkan wani yawace yawace,face masu zuwa aiki da kuma abin gaggawa.
Duk da haka,Maurizio Sarri ya umurci yan wasan shi da horo ranar laraba amma Ronaldo bai samu halattar horon ba saboda hadarin kamuwa da cutar.
Kungiyar juventus a shafinta na yanar gizo tace dan wasan mai shekaru 35 ya koma island din Madeira garin da aka haife shi, a lokacin yaduwar cutar ke kara kamari.
Coronavirus ta kashe kimanin mutane 4,400 tun lokacin da ta bayyana a watan disamba daya gabata,kuma ta rushe jadawalin kwallon kafa a fadin duniya.
An tsayar da wasan gida na Italy. Inter da Roma sun lura cewa an daga wasannin su tsakanin Getafe da Sevilla na gasar zakarun nahiyar turai wato  (Europa league) saboda matsalar tafiye tafiye da aka samu.
Wasan farko daya fara samun matsala a gasar Premier League ranar laraba ne tsakanin Manchester City da Arsenal da aka daga bayan wasu yan wasan Arsenal sun killace kansu.
Sauran wasannin guda biyu da suka rage a Spain na La liga za’a buga sune batare da yan kallo ba, wasannin faransa ma haka, an dakatar da masu zuwa kallon kwallo har izuwa 15 ga watan Afrilu.

 

Wannan maganar ta shafi masu buga wasan champions league da Europa league kamar yadda aka buga wasa na biyu wato (second leg  ) tsakanin Paris saint German da  Borussia Dortmund ba tare da yan kallo ba, Wanda hakan zai faru a yayin da Barcelona zata Kara da Napoli da kuma tsakanin Bayern Munich da Chelsea a kasar Germany.
Yan kallo baza su samu hallatar wasan Manchester United da Lask ba, Wanda za’a buga a Austria, da kuma Olympiacos da Wolves, da Wolfsburg da Shakhtar Domestk sai wasan Bayern Leverkusen da Rangers na Europa league.


© hutudole

Post a Comment

 
Top