A jiya Litinin 9 ga watan Maris na 2020 ne gwamnatin jihar Kano ta tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ta katse masa hanzarin cika daya daga cikin burinsa na karshe a rayuwa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Watanni shida da suka wuce, tubabben sarkin a wata hira da ya yi na domin bikin nadin sarautarsa a 2015 ya shaidawa manema labarai a fadar Sarkin Kano cewa burinsa na karshe a rayuwa shine ya mutu a matsayin sarki.

A ranar 4 ga watan Fabrairun 2015, Sanusi da ya zama sarki a ranar 8 ga watan Yunin 2014 ya ce,

"babu matsayin da ya fi kujerar Sarki."


Da ya ke magana a kan darajar da ya samu, Sanusi ya ce: "Ba ni da wani matsayi ko kadara. Addu'a ta shine daga fada a kai ni kabari na. Ba ni da wata bukata a rayuwa da ta wuce hakan. Na girma a fada kuma a gani na babu wani abinda ya fi sarkin Kano muhimmanci, kaka na da tsohon sarkin Kano.

"Mukami ba komi bane; abinda ke da muhimmanci shine aikin da ka yi. A karshe kowa yana son ya bar tarihi mai kyau. Ina son in yi aikin da al'ummar Kano za su cigaba da min addu'a bayan na mutu saboda jagoranci na gari da na yi.

"Babu wani gida da mutum zai so ya zauna da ya fiye fadar nan; Babu wani abu da mutum zai bukata a rayuwa da Allah bai bani ba."

Da ya ke amsa tambaya a kan yadda ya ji da masu zaben sarakuna suka zabe shi a matsayin Sarki, Sanusi II da aka haifa a ranar 31 ga watan Yulin 1961 ya ce abu ne mai wahala ya bayyana yadda ya ji.

Ya ce yana da matukar wahala mutum ya fadi yadda ya ke ji bayan an nada shi sarki amma ya kara da cewa Al-Kurani bai bar komai ba kuma kalaman da suka fi dacewa ko wane dan sarki ya fadi sune kalaman da Annabi Yusuf (AS) ya fadi bayan Allah ya ba daukaka shi da matsayi.

Ya ce: "Ya mahaifina, wannan shine abinda na gani a mafarki na; Allah ya kaddara aukuwar abinda na yi mafarki...' idan akwai wani abu da kowane musulmi ya yarda da shi shine Allah kadai ke bayar da mulki kuma Allah ne ya san dalilin da yasa ya zabe shi a wannan lokacin.'

Post a Comment

 
Top