Rahotanni dake fitowa daga garin Awe na jihar Nasarawa inda a nanne aka Ajiye Hambararren sarkin Kano inda  yake Samun Mafaka sun bayyana cewa akalla jami’an tsaro 40 ne ke tsare da sarkin.

 

A ziyarar da wakilin Punch ya kai gidan da ake tsare da hambararren sarkin Kanon wanda gidane ga shugaban karamar hukumar wanda kuma yana kusa da gidan Sarkin Awe din Ranar Laraba yace akwai jami’an tsaron ‘yansanda da DSS da Civil Defence duk a gurin.

 

Rahoton yace an kwacewa wakilin Punch dana Guardian wayoyinsu saboda zargin sun dauki hoton gidan da ake tsare da sarkin ba tare da izini ba amma daga baya an mayar musu da wayoyin inda aka bukaci su goge hotunan.

 

Rahoton ya kara da cewa, ba’a barin kowa ya ga Sarkin. Akwai wasu masu sarautar gargajiya su 2, Sarkin Karshi,Dr. Muhammad Bako da Yakanajin Uke, Alhaji Ahmad Abdullahi da suka je ganin Sarki Sanusi amma aka hanasu ganawa dashi.

 

Hakanan jami’an tsaro sun rika korar jama’ar da suka taru a wajan kofar gidan da ake tsare da sarkin.

 



© hutudole

Post a Comment

 
Top