Wadanda ake zargi da masu satar mutane ne a ranar Litinin da daddare sun sace daliban Rufus Giwa Polytechnic guda hudu a kan hanyarsu ta zuwa jihar Zamfara don halatar taron wayar da kai ga masu yiwa kasa hidma (NYSC) Wanda zai gudana a ranar talata.

 

Wadanda lamarin ya rutsa da su sun hada da maza uku da wata mata an sace sune a kusa da Funtua a cikin jihar Katsina da misalin karfe 11:30 na dare inda masu garkuwa da mutane dauke da makamai suka yi garkuwa da su a kan hanya.

 

Sakamakon wannan matakin, jami’an tsaro sun bada shawararsu ga masu ababen hawa don gujewa tafiye-tafiye a cikin dare musamman a wuraren da akwai barazanar tsaro.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

Emoticon
:) :)) ;(( :-) =)) ;( ;-( :d :-d @-) :p :o :>) (o) [-( :-? (p) :-s (m) 8-) :-t :-b b-( :-# =p~ $-) (b) (f) x-) (k) (h) (c) cheer
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.

 
Top