An dage duka gasannin UEFA, har da wasannin da za a yi a gasannin zakarun Turai na Champions League da Europa ran 17 da 18 ga wannan watan na Maris, saboda barkewar coronavirus.

Haka kuma na dakatar da fitar da jadawalin wasannin da za a buga, wanda da za a yi a 20 ga watan Maris.

An dage wasannin da za a yi tsakanin Manchester City da Real Madrid, da kuma Juventus da Lyon, da kuma Barcelona da Napoli da kuma tsakanin Bayern Munich da Chelsea a gasar Champions League a makon gobe.

An soke wasannin Manchester United da Wolves da Rangers a gasar Europa kamar yadda suka wallafa a shafinsu na Twitter.



© hutudole

Post a Comment

 
Top