Mutumin da ake ya madidi akan sa, ya zo ne dan ya gaishe da Shugaban kasa ne, Cewar Fadar Shugaban Kasa.

 

Mutumin da ake zargin ko ya kaiwa shugaban kasa hari a kebbi, ya so ne domin ya gashie da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

 

PREMIUM TIMES ta ruwaito lamarin wanda ya faru lokacin da Mista Buhari ya ziyarci Kebbi a ranar Alhamis.

 

Mai magana da yawun shugaban, Femi Adesina, a wata sanarwa ya ce ikirarin da da ake akan mutumin na kaiwa Shugaban kasa hari Karya ne.

 

Yayin da Shugaban kasa yake zagayen ganin buhunan shinkafa, tare da daukar hotuna tare da manoma, wani matashi yayi matukar farin ciki da ganin Shugaban nasa kusa. sai yayi yunƙurin zuwa wurinsa.

 

Bayan Jami’an tsaro sun hana saurayin, Sai ya fara zanga-zangar cewa a bar shi ya gaishe da Shugaban nasa. ” Mista Adesina ya ce.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top