Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bai wa duka ‘yan wasanta umarnin killace kansu bayan da wani dan wasan kwallon kwando na kungiyar ya kamu da cutar coronavirus.

Da ‘yan kwallon kafa da ‘yan kwallon kwando na kungiyar na amfani da ban daki guda, wanda hakan ya sa aka dage duka wasannin gasar La Liga tsawon mako guda.

Jami’an La Liga sun gana da Hukumar Kwallon Kafa ta Sufaniya (RFEF) da Kungiyar Kwallon Kafa ta Sufaniyar ranar Laraba da Alhamis kafin su yanke wannan hukuncin.

Dama dai Tawagar kwallon kafa ta Real Madrid din za ta fafata ne da Eibar a La Liga ranar Juma’a ba tare da ‘yan kallo ba.

Sufaniya na da sama da mutane 2,000 da suka kamu da cutar coronavirus.



© hutudole

Post a Comment

 
Top