Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule da sarakunan Lafiya da Awe sun ziyarci tubabben Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II a garin Awe.

 

Gwamnan ya isa Awe ne da missalin karfe 5:10 na yammacin yau Alhamis tare da Sarkin Lafiya inda suka ziyarci tsohon sarkin a masaukin baki na Shugaban Karamar Hukumar Awe inda Sanusi yake zaune bayan tube shi daga sarautada Gwamnatin Jihar Kano ta yi a ranar Litinin,kamar yanda Aminiya ta ruwaito.

 

Ziyarar Gwamnan ta kawo karshen jita-jitar da ake yadawa cewa an dauke tsohon Sarkin Kanon daga Awe.

 

Sai dai Aminiya ba ta samu bayani kana bin da Gwamnan da sarakunan suka tattauna da Sanusi II ba.



© hutudole

Post a Comment

 
Top