A jiyane muka ruwaito muku cewa hadimin shugaban kasa,Bashir Ahmad ya bayyana cewa shugaban kasa,Muhammadu Buhari ne ya baiwa Gwamnan jihar Kaduna umarnin baiwa hambararren sarkin Kano, Muhammad Sanusi II mukaman da ya bashi.

 

Bashir ya bayyana hakane a shafinshi na Twitter inda da dama sukace wannan batu ba gaskiya bane dan kuwa shugaban kasar ba shi da hurumin baiwa Gwamnan Umarnin yin hakan.

 

Bashir ya sake magana akan wannan batu inda yace kwankwaso yace Shugaba Buhari ne ya sa Ganduje ya cire Sarkin Kano kunce kun yadda gaskiya ya fada

 

Amma ni nace shugaba Buharine yasa Gwamnan Kaduna ya baiwa Sarki Sanusi II mukaman da ya bashi amma kunce baki yadda ba.

 

To kuwa kanku Adalci

 

Ya kara da cewa su wasu a gurinsu duk wani abu me kyau ba daga Buhari bane amma duk wani abu marar kyau daga wajansa ne.

 



© hutudole

Post a Comment

 
Top