Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NNPC) ta ce man fetur zai zama mai rahusa a Najeriya da zarar an kammala bututun mai na Ajakuta-Kaduna-Kano.
Manajan Daraktan Kamfanin na NNPC, Malam Mele Kyari ne ya bayyana hakan a ranar Lahadin da ta gabata a taron biki na 41 da aka gudanar a Kaduna, Kamar yadda jaridar Daily trust ta rawaito.
A cewar sa bayan kammaluwar aikin, zai kawo sauki da kuma rahusa hakan zai taimakawa kamfanoni da masana’antu  wajan kara kaimi gun gudanar da ayyukansu, wanda hakan zai Kara bada damar bawa matasa aikin yi don su dogara da Kansu.


© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top